14 Maris 2021 - 14:07
Olympic:An Sake Zaben Thomas Bach A Matsayin Shugaban Wasannin Olympic Na Wasu Shekaru 4

An sake zaben Thomas Bach a matsayin Shugaban hukumar wasannin Olympic na wasu shekaru 4 wato har zuwa shekara ta 2025.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an zabi Bach ne a wani taron Bidiyo da aka gudanar a ranar laraban da ta gabata, inda ya sami damar ci gaba da shugabancin wasannin Olympic har zuwa shekara ta 2025 ba tare da wata matsala ba.

Bach dan shekara 67 dan kasar Jamus kuma Lawya ya na shugabancin hukumar wasannin Olympic tun shekara ta 2013, sannan ya sami ci gaba da shugabancin hukumar kai tsaye ,inda ya sami kuriu 93 cikin kuri’u 94 da aka kada a zaben.

342/